Labarai

Faransa Zata Janye Sojojinta Daga Nijar – Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Faransa za ta janye sojojin da ta girke a Nijar a karshen shekarar 2023.

Macron ya ce sojojin Faransa 1,500 da aka tura a Nijar domin yaki da ta’addanci a yankin Sahel za su kasance.

“dawo cikin tsari” a ƙarshen shekara, kafofin watsa labarai na cikin gida sun ruwaito.

“Muna kawo karshen hadin gwiwar sojojin da muke yi da mahukuntan Nijar saboda ba sa son yakar ta’addanci,” in ji shi.

“Faransa za ta tuntubi gwamnatin mulkin soja don ganin an yi janyewar cikin lumana.

“Za mu ci gaba da tallafa wa nahiyar Afirka wajen yaki da ta’addanci, amma muna yin hakan ne kawai idan ya kasance bisa bukatar masu mulkin dimokuradiyya da hukumomin yankin,” in ji Macron.

Shugaban na Faransa ya kuma tabbatar da cewa jakadan Faransa a Nijar zai koma Faransa nan ba da jimawa ba.

Hukumomin soja a Nijar sun bukaci jakadan Faransa da ya fice bayan juyin mulkin, amma Faransa ta ki amincewa.

Daga nan ne gwamnatin mulkin sojan kasar ta ba da umarnin korar jakadan Faransa a karshen watan Agusta.

Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa ta yi tsami bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar.

Faransa ta dakatar da bayar da biza a Nijar tare da kwashe ‘yan kasarta, yayin da Nijar ta rufe sararin samaniyarta na jiragen sama masu rijista da Faransa.