El-Rufa’i Ya Gargadi ECOWAS Kan Daukar Matakin Soja A Nijar
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shawarci kungiyar ECOWAS da kada ta yi la’akari da tsoma bakin soja a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Tinubu, ya ce kungiyar ta yanke shawarar yin amfani da karfi a matsayin mafita ta karshe idan har jagororin juyin mulkin Nijar ba su mika mulki ga hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba.
Bayan wani taro da manyan hafsoshin tsaron kungiyar suka gudanar a Accra, babban birnin Ghana, ECOWAS ta bayyana a ranar Alhamis cewa ta fara aikin da take yi a Nijar.
Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau, El-Rufai ya yi ikirarin shiga tsakanin sojoji zai zama yaki ne tsakanin ‘yan uwa.
“Yayin da ECOWAS ke buga ganguna na yaki, na tuna da 1970s rock classic by Dire Straits – ‘Brothers in Arms’, domin yaki a yankin mu yaki ne tsakanin ‘yan’uwa.
“Hakika al’ummar Jamhuriyar Nijar daya ne da wadanda ke zaune a Arewacin Najeriya. Don haka mu karkata baya don mu guje wa wannan yaƙin basasa tsakanin ’yan’uwa,” ya rubuta.