Labarai

EFCC Tayi Dirar Mikiya A Babbar Hedikwatar Kamfanin Dangote

Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Alhamis, sun kai samame babban ofishin kamfanin Dangote a Legas.

Kamar yadda shafin jaridar TheCable ta ruwaito, jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun gudanar da bincike kan kudaden da aka ware wa kamfanin a zamanin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya CBN.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ki cewa komai kan wannan batun har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Sai dai wani ma’aikacin Dangote ya tabbatar da cewa jami’an EFCC sun shiga cikin babban ofishin kamfanin.

“Sun nemi takardu kan hada-hadar kudi da CBN,” in ji ma’aikacin.

Advertisement