EFCC Ta Gayyaci Ministar Da Aka Dakatar, Betta Edu

A bisa umarnin shugaban kasa Bola Tinubu, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta mika goron gayyata ga ministar jin kai da yaki da fatara da talauci, Betta Edu, da aka dakatar, bisa zarginta da hannu a badakalar karkatar da kudade da ta dabaibaye ma’aikatar.

A yanzu ana sa ran hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar za ta fara gudanar da bincike a hukumance kan batutuwan da suka shafi yadda ake fitar da kudaden da ake son kaiwa ga yan Najeriya domin yaki da fatara.