Labarai

EFCC Ta Cafke Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika Kan Ɓatar Biliyan N8

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta cafke tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, bisa zargin almundahanar Naira biliyan 8, inji rahoton PUNCH.

Majiyar EFCC ta shaida wa jaridar cewa tsohon ministan ya isa ofishin hukumar da ke Abuja ranar Talata a wani bangare na binciken damfarar da faru ma’aikatar da ke karkashin sa a wancan lokaci.

Sirika, kamar yadda majiyar ta bayyana, EFCC ta gayyace shi ne kan badakalar bada kwangila ga wani kamfani, Engirios Nigeria Limited, mallakin kanin sa, Abubakar Sirika.

A ‘yan watannin da suka gabata ne dai aka yi wa tsohon ministan bincike a kan yadda ake tafiyar da aikin jirgin Najeriyar da bai yi nasara ba a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Advertisement