Dubun Wani Dan Ta’adda Ta Cika, Dubi Tarin Makaman Shi

An kama James Peter, wani gawurtaccen wani dan ta’adda ne, wanda ya addabi jihohin Rivers da kuma Bayelsa da Garkuwa da mutane da kuma sata.

James peter dai dan karamar hukumar mulkin Southern Ijaw ne, dake jihar Bayelsa, kuma yaren kabilar IJAW ne shi.

Shine ya addabi jihar Rivers da kuma Bayelsa da garkuwa da mutane, wanda yasa har ake cewa fulani ne ke wannan ta’asar kafin cafke.

ku dubi irin makaman da ake zargin cewa an karbo hannunsa.