DSS Ta Kame Shugaban Miyetti Allah Bisa Kafa Kungiyar ‘Yan Banga

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan kirkiro wata kungiyar ‘yan banga ta Fulani mai suna Nomad’s Vigilante Group.

Koda yake mai magana da yawun DSS, Dr Peter Afunanya, bai tabbatar ko musanta rahoton ba, jaridar LEADERSHIP ta tattaro cewa an kama Bodejo ne a kwanakin baya a babban ofishin Miyetti Allah da ke Tundun Maliya Cattle Market, Kilomita 22, Babban Titin Abuja-Keffi, Tundun-Wada. Karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Shaidun da suka yi tsokaci a shafukan sada zumunta, sun ce jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya, sun kai farmaki a ofishin Miyetti Allah da ke kusa da Cocin Goshen, da misalin karfe 3:40 na yammacin ranar Talata, inda daga nan ne suka tafi bayan sun kama Bodejo a kofar gidan.

An kama Bodejo ne saboda fargabar cewa kirkiro kungiyar ‘yan banga ta Fulani, Nomad na iya haifar da tashin hankali a fadin kasar nan gaba.