DSS Ta Kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kamar yadda jaridar PM ta ruwaito.

An kama shi ne jim kadan bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu yayi masa a daren Juma’a.

Sai dai jaridar ta yi shiru kan inda jami’an ‘yan sandan sirri suka dauke Gwamnan CBN.

Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar, ya umurci Emefiele da ya mika aikinsa ga mataimakin gwamnan babban bankin CBN mai kula da ayyuka har sai an kammala bincike a kan sa.

A watan Janairu ne dai babban alkalin babbar kotun tarayya mai shari’a John Tsoho ya hana hukumar DSS tsarewa ko kuma kama gwamnan babban bankin kasar bisa zargin bada tallafin ta’addanci.

Daga nan ne dai hukumar ta DSS ta yi kokarin cafke ma’aikacin banki dan asalin jihar Delta amma tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga tsakani ya dakatar da hukumar.