Daraktan Fina-Finai A KannyWood, Aminu S Bono Ya Rasu

Daga Allah muke, sannan kuma a gare Shi zamu koma!

Allah Ya yiwa shahararren daraktan fina-finan Hausa a masana’antar KannyWood Aminu S Bono rasuwa.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta KannyWood, Abba El-Mustapha ya sanar rasuwar tasa a shafin shi na Facebook da yammacin Litinin (20/11/2023.

Lokacin ake gudanar da Jana’izar Aminu S Bono| Abba El-Mustapha a tsakiyar jama’a.

Muna addu’ar Allah Ya jikan shi, Ya kuma gafarta masa zunuban shi, yasa aljanna ce makomar shi tare dukkan yan uwa musulmai da suka riga mu gidan gaskiya. Idan kuma tamu ta zo Allah yasa mu cika da mani.