Dalilin Da Yasa Hancin Mace Ke Ƙara Girma Da Kumburin Ƙafafu Idan Tana Da Ciki
A dabi’ance dukkan mata suna samun nau’o’in sauye-sauye a jikin su a lokacin da suke da juna biyu, kuma wasu daga cikin wadannan sauye-sauye na iya zama abin ban mamaki da kuma bayyananne abu, a cikin wannan makala za mu yi nazari kan abin da ke kara girman hancin mace a lokacin da take da juna biyu.
Kamar yadda wani rubutu da aka rubuta a shafin yanar gizo na healthline.com ya bayyana cewa, babban abinda ke haifar da hakan shi ne sinadarin daukar ciki, domin a lokacin da mace take da juna biyu jikin ta na samun sauye-sauye da yawa na hormonal, kuma manyan kwayoyin halittar biyu sune Estrogen da progesterone.
Wannan hormone da aka fi sani da estrogen yana kara yawan jini a ko’ina a jikin ta, wannan shi ne yake haifar da kumburi a wasu sassan jikin ta kamar hannayen ta, kafafuwa, wuyan ta, da kuma mafi shaharar hancin ta, wanda ke haifar da fadadawa.
An ce mace mai ciki za ta samu karin isrogen fiye da yadda za ta samar a duk tsawon rayuwar ta idan ba ta da juna biyu, wannan karuwar da ake samu a lokacin daukar ciki ne ke ba wa mahaifa damar fitar da abinci mai gina jiki don tallafawa cigaban jariri da kuma inganta samuwar jini.