Labarai

Daliban Jami’ar Zamfara 2,565 Sun Fice Kan Karin Kuɗin Makaranta

Shugaban kungiyar daliban jihar Zamfara na Jami’ar Tarayya ta Gusau, ZAMSSA, Kwamared Haliru Ibrahim, ya koka kan yadda dalibai sama da 2,565 ba za su iya ci gaba da karatu ba saboda karin kudin makaranta.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai a jami’ar, babban birnin jihar.

Ya bukaci Gwamna Dauda Lawal da sauran masu ruwa da tsaki da su yi tanadin yadda ya kamata domin taimakawa dalibai ‘yan asalin jihar.

Ya ci gaba da cewa cire tallafin man fetur da kuma wahalhalun da ake fama da su a halin yanzu na taka muhimmiyar rawa wajen barin daliban musamman a jami’ar tarayya ta Gusau.

Ya bukaci daliban da su samu ayyukan yi na wucin gadi domin tallafa musu.