Boko Haram Vs ISWAP: Ƴan Ta’adda 60 Sun Mutu A Rikicin Shugabanci
Akalla ‘yan ta’adda 60 ne rahotanni suka ce an kashe a wani sabon fafatawa da mayakan Boko Haram suka yi da mayakan kungiyar ISWAP a jihar Borno.
Wani kwararre a fagen yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na X, wanda a baya Twitter, a ranar Asabar.
Ya ce an gwabza kazamin fada tsakanin kungiyoyin biyu a tsibirin Tumbum Ali da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno da misalin karfe 2:00 na rana, inda aka kashe kwamandojin kungiyoyin biyu a yakin.
Makama ya kara da cewa rikicin ya biyo bayan kashe mayakan ISWAP da ‘yan kungiyar suka yi a baya bayan nan a farmakin da suka kai maboyarsu a yankin.
Kungiyoyin ta’addancin biyu dai sun sha gwabza fada a kan sabanin akida da wasu dalilai a baya.
Ya rubuta cewa: “An kashe dimbin mayaka daga Jam’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihd, Boko Haram, da kuma Daular Islama ta Yammacin Afrika, ISWAP, ‘yan ta’adda, ciki har da kwamandojinsu a lokacin wani hari da aka kai musu. rikicin cikin gida a Arewa maso Gabashin jihar Borno.
“Rahotanni sun nuna cewa an gwabza kazamin fada tsakanin kungiyoyin biyu a tsibirin Tumbum Ali dake karamar hukumar Marte da misalin karfe 1400.
“Majiyoyin leken asiri sun bayyana cewa an lalata kwale-kwale guda shida na kungiyar Bakura Buduma da na JAS element guda hudu, dukkansu cike da mayaka.
“Majiyoyin sun ce wadanda suka jikkata a bangarorin biyu na iya zarta fiye da 60 yayin da ake ci gaba da gwabza fada.”