Bello Turji Ya Saki Sabon Hoton Shi Sanye Da Kakin Jami’an Tsaro

Shahararren shugaban yan bindiga dake addabar yankin arewa maso yammacin kasar nan, Bello Turji Kachalla, na cigaba da gujewa jami’an tsaron Najeriya, da kuma kai hare-hare a kauyukan Zamfara, Sokoto, Niger da Katsina.

Hotunan nasa na baya-bayan nan sun bayyana inda aka gan shi shi sanye da kakin jami’an tsaron Najeriya, yayin da yan kungiyar sa ke gefensa suna riƙe da nagartattun bindigogi.

Wani abin da ka iya daukar hankulan mutane shi ne yadda yan bindigan nan da suka yi kaurin suna suka zauna cikin kwanciyar hankali a kan wata kujera ta roba sanye da kaki.

Jajircewar Turji wajen kalubalantar jami’an tsaro abin damuwa ne idan aka yi la’akari da halin da ƙungiyar ke ciki.

Bello Turji ya jagoranci hare-hare da dama a kan al’ummar Zamfara a shekarar 2021 wanda ya haifar da tabarbarewar tattalin arziki da kuma tabarbarewar al’umma a jihar da ma makwabtanta.

Hakan yasa gwamnatin tarayya ta tura karin jami’an tsaro domin magance ta’asar da yan bindigar ke aikatawa.

Yan bindigar sun zama daya daga cikin manyan kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Yamma. Akwai kungiyoyin yan bindiga da dama da ke ta’addanci a yankin amma jami’an tsaro sun yi nasarar kashe da dama daga cikin wadannan masu aikata laifuka.

Sai dai Bello Turji da wasu yan kungiyarsa har ana neman su ruwa ajallo.