Ban Canja Matsayi Ba Kan Falasɗinu – El Ghazi Bayan Soke Kwantiraginsa Kan Rubutu A Soshiyal Midiya

Dan wasan kwallon kafa na Dutch Anwar El Ghazi ya ce kawo karshen kwantiraginsa da kulob din Mainz 05 na Jamus “ba komai ba ne idan aka kwatanta da wutar jahannama da ake yiwa marasa laifi da masu rauni ba a Gaza”.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, Mainz ta ce an kawo karshen yarjejeniyar El Ghazi ne saboda “samun tsokaci da rubutu daga dan wasan a shafukan sada zumunta”.

El Ghazi dai ya aike da sakonnin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu kuma ya tsaya kan kalamansa bayan da Mainz ya dakatar da shi.

“Ba na nisantar da kaina daga abin da na fada ba kuma na tsaya ne ga bil’adama da kuma bangaren wadanda ake zalunta har sai ranar karshen numfashi na,” in ji El Ghazi.

Kasar Jamus ta kara nuna rashin hakuri da kalaman goyon bayan Falasdinu, kuma masu gabatar da kara na Jamus sun ma kai ga zargin El Ghazi da “dagula zaman lafiyar jama’a ta hanyar amincewa da aikata laifuka tare da tunzura kiyayya”.