Labarai

Bafarawa Ya Juya Akalar Biliyan N4.6 Daga Sambo Dasuki – Shaida A Kotu

Wani mai gabatar da shaida na biyu, PW2, a shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, Kassim Yusuf, a ranar Talata, ya sake bayyanawa a gaban mai shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja cewa tsohon gwamnan ya karkatar da wasu makudan kudade da suka kai naira biliyan N4,000,600,000 da ya karba a matsayin asusun tsaro daga ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Kanar Sambo Dasuki.

Hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, na tuhumar Bafarawa a kan wasu tuhume-tuhume 25 da aka yiwa gyaran fuska, wadanda suka hada da zamba cikin aminci da karkatar da kudaden jama’a har Naira biliyan N4.6.

Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Bashir Yuguda, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, Dalhatu Investment Limited da Sagir Attahiru (ɗan Bafarawa, kuma tsohon ɗan takarar mataimakin gwamnan Sakkwato a jam’iyyar PDP a 2023).

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, shaidan, wani jami’in EFCC, wanda lauyan masu shigar da kara, Rotimi Jacobs, SAN ya jagoranta a gaban kotu, ya shaida wa kotun cewa biliyan N4.6 kudaden tsaro da Dalhatu Investment Limited ya karba daga Sambo Dasuki an yi amfani da su wajen daukar nauyin ’yan asalin Jihar Sakkwato zuwa aikin Hajji.

Ya kara da cewa, an kuma yi amfani da wani bangare na kuɗin ne wajen neman takarar shugabancin kasa a shekarar 2015 da Bafarawa yayi, da kuma biyan bashi a kasashen waje, da kuma sayen motoci masu tsada da suka hada da Lexus, Toyota Hilux pickups da motoci 16 Peugeot 206 ga jam’iyyar PDP da shugabannin kananan hukumomi a jihar.

Shaida na ya kuma bayyana cewa an bada Naira biliyan N1 daga cikin kudaden zuwa kusan masu canjin kudaden waje 10 (Bureau De Change, BDC) don canza su zuwa dalar Amirka.

“Kimanin BDC guda 10 ne suka ce Dalhatu Investment Limited ya aika wani ya karbo kudin kuma an tura kimanin Naira miliyan N800 zuwa asusun Dalhatu Investment Ltd domin a mayar da su dala. An kuma biya wani kamfani mai suna Development Strategy International Ltd.

“Daraktocin kamfanin su ne Islam Wali da Muhammad Wali wadanda ‘yan uwan Ambasada Sanata Abdullahi Wali ne,” kamar yadda ya shaida faɗawa kotun.