‘Auren Mace Da Mace, Namiji Da Namiji’ Aƙidar Sheɗan Ce Ba Kiristanci Ba – Olumba

Shugaban Cocin kungiyar ‘yan uwa ta Cross and Star, Olumba Olumba Obu yayi Allah-wadai da shigar auren jinsi da wasu kungiyoyin addini suka yi a cikin al’umma, yana mai cewa akidar sheɗan ce.

Ya ci gaba da cewa ba koyarwar Yesu Kiristi ba ce, kuma yayi kira ga dukan ’yan Adam, musamman Kiristoci su nisan ce ta.

Hakan na kunshe ne a sakonsa na Kirsimetin 2023 da ya fitar a hedkwatar kungiyarsa, da safiyar Litinin.

Ya ce, “Duk mai yin saɓanin abin da Yesu Kiristi ya koyar, yana cika koyarwar Iblis ne, ba na Almasihu ba. Allah ya dawo da ’yan adam da halitta zuwa yanayin adalci, tsarki da karamci.

“Ya kamata Kiristoci su guji soma koyarwa da ayyuka na bare da suka saɓa wa nufin Allah ga ’yan Adam.

Yayi gargaɗi cewa yayin da Kiristoci a duk faɗin duniya suke bikin Kristi, ya kamata a ƙyale koyaswarsa daba ta da tushe ta a fitar da ita a zukatan amintattunsa.

Ya tuna cewa Yesu Kristi ya zo ne domin ya cika dokoki da kamar sauran annabawa kuma ya sake tabbatar da tsarkin aure ya zama tarayya tsakanin namiji da mace kawai, waɗanda za su zama kungiya ɗaya.