An Yanke Wa Tsohon Shugaban Kasa Hukuncin Ɗaurin Rai-Da-Rai A Gidan Yari

An jefa tsohon shugaban Jamhuriyar Comoros Ahmed Abdalla Sambi gidan yari har tsawon rayuwar shi bayan da aka same shi da manyan laifuka da ya aikata a lokacin da yake kan mulki.

Kotun tsaro ta kasa, babbar kotun kasar wacce ba za a iya sauya hukuncin ko kuma a daukaka karar hukuncin ta ba, ta jefa tsohon shugaban kasar mai shekaru 64 a gidan yari.

An yanke masa hukuncin ne da laifin sayar da fasfo ga wadanda ba yan kasa ba da ke zaune a yankin teku, sannan kuma an zarge shi da zambar miliyoyin daloli daga asusun gwamnati.

Da ya ke bayar da misali da wani zaman da aka yi na rashin adalci, tsohon shugaban ya fusata ya ki halartar zaman kotun a matsayin shi na kotun tsaron kasar. Tuni dai Sambi ya shafe shekaru hudu a gidan yari kafin ya fuskanci shari’a da kuma yanke masa hukuncin daurin.

Ta bakin lauyoyin shi, Sambi ya bayar da hujjar cewa, babu wata shaida da ke nuna cewa an wawure kudaden jama’a bayan da ya zartar da dokar da ta ba da izinin sayar da fasfo na Comoros ga mutanen da ba su da wata kasa a yankin teku akan kudi.