Labarai

An Yanke Wa Matashi Hukuncin Daurin Shekaru 90 A Gidan Yari

Wata kotu a Kenya ta yankewa wani dan kasar Kenya mai suna Chris Wanjala dan shekaru 24 hukuncin daurin shekaru 90 a gidan yari.

Wannan na zuwa ne bayan da aka same shi a ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu da laifin kisan gillar da aka yi wa wata ‘yar kasar Sweden mai mishan Lilian Bourcart mai shekaru 74.

Wanjala wanda dan kasar Sweden mai wa’azin bishara ta dauka aiki, an same shi da laifin yin fashi da makami, fyade da kashe tsohowar wacce ta dauke shi aikin kula da gidan yara kuma ya gudanar da aikin agaji a gidan Milimani da ke Kitale, gundumar Trans Nzoia a Kenya.

Rahotanni sun ce ya aikata laifin ne shekaru biyu da suka wuce. Alkalin kotun Julius Ng’arng’ar wanda ya yanke wa Wanjala hukuncin daurin shekaru 90 a gidan yari, ya ce hukuncin ya zama dole idan aka yi la’akari da irin zaluncin da aka yi amfani da shi wajen aikata laifin.

An dage yanke hukuncin wanda suka aikata laifin tare da Wanjala, Dominic Nyongesa, har sai an tantance shekarun shi.

Mai gabatar da kara a nata bangaren, ta ce wadannan biyun sun cancanci hukuncin daurin rai-da-rai tun da laifin kisa ne, domin ya zama darasi ga wasu.