Labarai

An Tura Yar TikTok, Ramlat Princess Gidan Yari Bisa Zargin Yaɗa Maɗigo

Kotun Shari’ar Musulunci dake Kano ta tasa keyar jarumar TikTok Ramlat Mohammed (wacce aka fi sani da Princess) zuwa gidan yari kan zargin badala, maɗigo da karuwanci.

A ranar Juma’a ne Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa na kotun Musuluncin dake unguwar Sharada yasa ajiye Ramlat Princess a gidan yari bayan Hukumar Hisbah ta gurfanar da ita a gabanta.

A kwanakin nan ne wani bidiyon Ramlat Princess ta ya karade shafukan sada zumunta, Facebook, Twitter, Instagram wanda a ciki take tallata madigo, har ta bayyana kanta a matsayin mai wannan muguwar dabi’ar a zahiri.

A cikin bidiyon, an ji matashiyar na cewa, duk wanda ai aure ta, to dole sai ya amince cewa ita za ta auro tata matar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Takardar karar ta bayyana cewa an sami jarumar Tiktok din tana yin amfani da kafar sada zumunta tana yin kalaman badala.

A cewar takardar kara laifukan da ake zargin ta da su laifuka ne da suka saba da sashe na 341 da 275 da 227 na Kundin Penel code

Wacce ake zargin ta amsa laifukan inda ta nemi afuwar kotu bisa laifukan da ta aikata.

Sai dai saboda kurewar lokaci kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 19 ga Fabrairu don yanke hukunci.

Haka kuma kotun ta yi umarnin tisa keyar Ramla zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a sake dawowa gaban kotun.

Wannan na zuwa ne bayan wata kotun Musulinci a jihar ta yanke hukuncin daurin wata shida kan laifin badala ga wani mai suna Murtala Adamu, wanda aka kama tare da fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.

Kotun da ke unguwar Gama ta bai wa matashin zabin biyan tarar N30,000 kan laifin tayar da haniya da aikata badala.

An yanke masa hukuncin ne washegarin da kotun ta sa a tsare Murja a gidan yari kan laifin badada da koyar da karuwanci.

An gurfanar da Murja ne bayan an kama su da Murtala Adamu a unguwar Hotoro, bayan jami’an Hukumar Hisbah Kano, sun kai samame sakamakon korafin da mazaunar unguwar suka shigar.

Murja dai ta musanta zargin da ake mata na koyar da karuwanci, badala, da kuma tayar da hankali jama’a.