An Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Bilyaminu Moriki

‘Yan majalisa 18 daga cikin 24 na majalisar dokokin jihar Zamfara sun tsige kakakin majalisar, Hon. Bilyaminu Moriki.

Sai dai ‘yan majalisar sun amince da Hon. Bashar Gummi a matsayin kakakin majalisar sabo.

DAILY POST ta tattaro cewa mambobi 18 daga cikin 24 sun amince da tsige shugaban majalisar a wani taron gaggawa da suka yi a daren ranar Alhamis.

Wannan kafar yada labarai ta kara da cewa, watakila tsige shugaban majalisar bai rasa nasaba da kudirin da daya daga cikin ‘yan majalisar da ke wakiltar mazabar Maru, Hon. Nasiru Abdullahi ya gabatar.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa tsige shugaban majalisar ya biyo bayan sake bullar matsalar rashin tsaro ne sakamakon ci gaba da kai hare-hare da ‘yan bindigar ke kaiwa al’umomin jihar.

DAILY POST ta tattaro cewa shugaban majalisar da aka tsige ya yi kwanaki a jihar kafin a tsige shi.

A cewar Hon. Shamsudeen Basko mai wakiltar Talata Mafara, ‘yan majalisar sun shaida wa sabon shugaban majalisar cewa batun rashin tsaro na daya daga cikin muhimman batutuwan da ya kamata a baiwa fifiko, wanda ya kai ga tsige tsohon shugaban majalisar.

Ya kara da cewa, “Ina da batutuwa guda biyu amma an yi nazari a kan daya, wato na rashin tsaro, wanda ya dagula al’ummar Zamfara, ana kashe wasu da sace su.

“Ya kamata mu tashi tsaye mu yi wani abu don kare mutanenmu saboda ‘yan bindigar da ke dauke da makamai suna mamaye hedikwatar kananan hukumomin ba tare da fuskantar kalubale ba.

“Muna kira ga gwamnati da ta dauki mataki yanzu don kare mutanenmu.”

A halin yanzu, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, baya jihar.