An Tsare Ni, Yankin Sahel Zai Iya Komawa Ga Rasha – Inji Bazoum
Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, yayi kira da a kawo karshen juyin mulkin da ya tsige shi daga mukamin shi.
Da yake bayyana kansa a matsayin wanda aka yi garkuwa da shi, Bazoum yace yana cikin ‘yan Nijar masu yawa da gwamnatin mulkin sojan kasar ta daure ba bisa ka’ida ba.
A cikin wani shafi a jaridar Washington Post, Bazoum ya koka da cewa yankin Sahel na iya fadawa hannun Rasha.
Yayi kira ga gwamnatin Amurka da daukacin al’ummar duniya da su taimaka wajen dawo da tsarin mulkin kasar.
Jami’an tsaron fadarsa sun hambarar da gwamnatin Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.
Duk da haka, tsohon shugaban ya rubuta: “Na rubuta wannan a matsayin garkuwa.
“Nijeriya na fuskantar hari daga gwamnatin mulkin soja… kuma ni daya ne daga cikin daruruwan ‘yan kasar da aka daure ba bisa ka’ida ba.”
“Dole ne a kawo karshen juyin mulkin, kuma dole ne gwamnatin mulkin soja ta sako duk wanda suka kama ba bisa ka’ida ba.
“A yankin Sahel da ke fama da rikici a Afirka, Nijar ta kasance tushe na karshe na mutunta ‘yancin ɗan adam a cikin ƙungiyoyin kama-karya da suka mamaye wasu maƙwabtanmu.
“Dukkan yankin Sahel na iya fadawa cikin tasirin Rasha ta hanyar kungiyar Wagner, wacce ta’addancin ta ya kasance cikakke a Ukraine.”
Bazoum ya lura cewa ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram “tabbas za su yi amfani da rashin zaman lafiya a Nijar, tare da yin amfani da ƙasar a matsayin matattakalar kai hare-hare a maƙwabta da kuma lalata zaman lafiya, aminci da ’yanci a duniya.