An Saki Wata Amarya Wajen Daurin Aure, Bayan Angon Ya Ga Wasu Hotunan Ta

An saki wata amarya kim kadan bayan a dauren su da abin kaunar zuciyar ta.

An bayyana cewa bayan daura aure masu taya ma’auratan murnar suna cikin hidimar bikin sai a baiwa angon kyautar fure da wani abu boye a cikin furen, wanda angon ya fara sake-sake a cikin ran shi.

Bayan wani dan lokaci sai angon ya fice daga wajen bikin inda ya shiga cikin wani daki domin duba abina yake cikin wannan ambulan.

An bayyana cewa hotunan amaryar ne a tsirara wani wanda ake zargin tsohon saurayin ta ne ya baiwa angon.

Saboda munin hotunan a tsakiyar bikin da dare angon ya kasa daurewa inda nan take ya fidda sanarwar cewa ya saki amaryar.

Wannan labarin bayar da a cikin wata shafin intenet mai suna: Life In Saudi Arabia, ma’ana rayuwa a Saudi Arabia.