An Naɗa Janar Nguema Shugaban Rikon Kwarya Na Gabon Bayan Juyin Mulki

An nada Janar Brice Oligui Nguema, shugaban jiga-jigan ‘yan Republican Guard na Gabon – sashin da ke kula da tsaron shugaban kasar – a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar.

Sanarwar a ranar Laraba ta zo ne sa’o’i bayan sanarwar kwace mulki da sojoji suka yi a gidan talabijin na gwamnati wanda shi kansa ya biyo bayan ayyana nasarar da hukumar zaben kasar ta yi wa Shugaba Ali Bongo a zaben na ranar Asabar.

Bongo ya samu kashi 64.27 cikin 100 na kuri’un da aka kada, zaben da ‘yan adawa suka ce “magudi ne” da Bongo da magoya bayansa suka shirya. Dan takarar adawa Albert Ossa wanda ya wakilci hadewar jam’iyyu shida ya zo na biyu da kashi 30 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Nguema na daya daga cikin masu fada a ji a kasar kuma ana kyautata zaton yana da alaka da hambararren shugaban kasar. A matsayinsa na dan hafsan soja, tun yana karami ya kasance yana sha’awar shiga aikin soja kuma ya samu horo a makarantar horas da sojoji ta masarautar Meknes da ke kasar Morocco.