An Kama Mutumin Da Ya Tayar Da Gobarar Da Ta Kashe Mutane 77 A Afrika Ta Kudu

‘Yan sandan Afirka ta Kudu sun kama wani mutum da ake zargi da tayar da gobarar da ta kashe mutane da dama a wani gini da ke tsakiyar birnin Johannesburg a shekarar 2023.

‘Yan sanda sun tabbatar da kama shi a ranar Laraba, kwana guda bayan wanda ake zargin mai shekaru 29 a duniya ya shaidawa wani bincike kan gobarar cewa yana da hannu wajen tada wutar.

Ana sa ran mutumin zai gurfana a gaban wata kotun Johannesburg nan bada jimawa ba, bisa zarginsa da aikata laifin kone-kone, laifukan kisan kai na mutane 77 da kuma mutane 120 a matsayin wadanda yayi yunkurin kashewa, in ji ‘yan sanda a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato.

Gobarar da ta tashi a ranar 31 ga Agusta, 2023, ta kama ginin Usindiso mai hawa biyar a Marshalltown a cikin birnin Johannesburg.