Labarai
An Kama Matar Tsohon Shugaban Kasar Zambia Bisa Zargin Sata
‘Yan sanda a Zambiya sun kama matar tsohon shugaban kasar Edgar Lungu bisa zarge-zarge uku da suka hada da satar wata mota da ta musanta.
An kama Esther Lungu wadda a halin yanzu take tsare a babban birnin kasar, Lusaka, tare da wasu mutane uku.
Kakakin ‘yan sandan Danny Mwale ya tabbatar a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa an kuma tuhumi mutanen hudu da laifin satar takardar shaidar mallakar wata kadara a Lusaka.
Ana kuma tuhumar su da mallakar kadarori da ake kyautata zaton samun kudin shiga ne.
A halin yanzu dai ana gudanar da bincike kan wasu tsoffin ministoci da jami’an gwamnati da kuma iyalan Mista Lungu bisa zargin aikata laifuka.
Dukkansu sun musanta aikata ba daidai ba.