An Kama Dattijo Mai Shekaru 67 Bisa Lalata Yarinya Ƴar Shekara 3 A Adamawa

Wani dattijo mai shekaru 67, Mahmudu Adamu, ya amsa laifin lalata da akalla ‘yan mata uku masu karancin shekaru ta hanyar cusa yatsunsa a al’aurarsu a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Adamu wanda a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda, ya ce yana samun mafi girman jin dadin jima’i daga sanya yatsunsa a al’aurar kananan yara mata, masu shekaru tsakanin hudu zuwa sha daya.

Rahotanni sun bayyana cewa Adamu ya lalata yaran ne a gidansa da ke Sabon Layi a karamar hukumar Ganye a jihar, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguorje, yayin da yake tabbatar da kama shi ga SaharaReporters a ranar Alhamis, ya ce Adamu ya amsa laifinsa.

“Ya furta cewa yana samun gamsuwa ta hanyar sanya yatsunsa cikin al’aurar kananan ‘yan mata, ya ce yana jin gamsuwa da jima’i a duk lokacin da ya saka yatsa cikin wacce abin ya shafa.

“An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton iyayen wacce aka lalata ta uku.

“Kwamishanan ‘yan sanda, Afolabi Babatola, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na gaskiya tare da gurfanar da wanda ake zargin bayan an kammala bincike,” in ji Nguroje.