An Dakatar Da Kwamandan Yan Sakai Na Jihar Zamfara, Kanar Rabi’u Garba

Gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Kanar Rabi’u Garba (mai ritaya), kwamandan sabbin yan sakai na jihar.

Sanarwar dakatarwar ta fara aiki ne nan take a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Nakwada ya fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Wannan don sanar da jama’a ne cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da nadin Kanal Rabiu Garba a matsayin Kwamandan Rundunar Tsaron yan sakai ta Jihar.

“Dakatar ta fara aiki nan take.”

Yayin da sanarwar ba ta fayyace dalilin dakatar da Garba ba, ana kyautata zaton hakan na da alaka da kalaman da ya yi a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo.

A cikin hirar, Garba ya soki gwamnatin jihar kan yadda ta gaza samar da isassun kudade ga hukumar ta yan sakai tun bayan kafa ta a farkon wannan shekarar.

Ya yi nuni da cewa, yan sakan ba su samu tallafin kudi daga gwamnatin jihar ba tun kafuwarta a watan Janairu.

Ya kuma kara da cewa, duk da an kaddamar da yan sakan watanni hudu da suka gabata, sau daya ne kawai suka karbi albashinsu kuma suna fuskantar kalubale saboda rashin kudi, ciki har da gazawar gwamnatin jihar wajen samar da man fetur ga motocin sintiri.

“An biya mu alawus-alawus din mu sau daya kacal tun lokacin da muka karbi aikin watanni hudu da suka wuce,” in ji shi.

Garba ya kuma bayyana cewa rashin kudi da tallafin kayan aiki ya yi matukar tasiri wajen yaki da ‘yan fashi yadda ya kamata.

Ya soki gwamnati kan yadda yan sakai za su yaki masu aikata laifuka ba tare da isassun kudade ba, inda ya bayyana cewa shi da kan sa ya karbi Naira N98,000 kacal tun hawansa muƙamin, kuma yana amfani da kudinsa wajen siyan man fetur wajen gudanar da ayyuka.

“Rashin kudi da sauran kayan aiki ne ke da alhakin rashin gudanar da ayyukan mu.

“Kun horar da wani, kun ba shi bindiga don yakar masu laifi, sannan kuka ki biyansa alawus dinsa na wata-wata, kuma ba za ku iya mai da motarsa ​​ba. Yaya kuke tsammanin zai yi?

“Na rantse da Allah tun lokacin da na hau ofis a watan Janairu na wannan shekara a matsayina na kwamanda na jihar, na samu Naira 98,000 kacal.

“Haka zalika, ni kan sayi mai da kudina a duk lokacin da za mu fita aiki.

“Wannan ba zai taba faruwa a ko’ina a duniya ba.” Ya kara da cewa.

Kwamandan ya kuma zargi wasu mutane a cikin gwamnati da yin zagon kasa ga kokarin Gwamna Dauda Lawal na yaki da ‘yan fashi.

Duk da kokarin isar da wadannan al’amura ga gwamnan da sauran jami’ai, ya yi ikirarin cewa ba a dauki matakin magance koke-koken su ba.

Garba ya ci gaba da cewa, “Na san mai girma Gwamna Dauda Lawal ya jajirce sosai wajen yakar ‘yan fashi amma akwai wasu mutane a majalisarsa da ke yi masa zagon kasa saboda dalilai na son rai.

“Na yi kokarin tuntubar gwamnan domin sanar da shi halin da muke ciki, amma bai samu damar zuwa ba.

“Na tuntubi wasu fitattun malaman addinin Musulunci a jihar irin su Sheikh Ahmed Umar Kanoma da Sa,idu Maikwano, wadanda na yi tunanin za su iya magana da gwamnan kan lamarin, amma abin takaici babu wani ci gaba.”

Ya yi gargadin cewa idan lamarin bai inganta ba, za a tilastawa mambobin kungiyar yan sakan yin murabus.