Labarai
An Ciro Harsashin Bindiga AK-47 Guda 38 Daga Cikin Ido Na – El-Zakzaky
Da alamu har yanzu shugaban kungiyar yan shi’a ta Najeriya, Sheikh Yakubu Ibrahim El-Zakzaky bai manta tashin hankalin da ya afka masa da mabiyan shi ba wanda yayi sanadiyar ji masa rauni da kuma asarar rayuka da da dama a Zaria ba.
Idan ba’a a manta ba, sojojin Najeriya da mabiyan El-Zakzaky sun yi wata mummunar arangama a garin Zaria, jihar Kaduna a gab da karshen shekarar 2015, lokacin mulkin janaral Muhammadu Buhari.
Bayan dawowa da jinya a kwanan, jagoran shi’ar, ya bayyana cewa, likita ya duba cikin kansa, kuma ya gano a ciro alburusai sama da 38 a cikin kwayar idonsa, malamin ya bayyana haka ne cikin wani faifayin bidiyo da aka nada yayin da yake jawabi ga mabiyansa.