An Cafke Wata Mata Bisa Zargin Kashe Mijinta Da Wuƙa A Bauchi

Jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi sun cafke wata matar aure mai suna Maimunatu Sulaiman ‘yar shekara 21 da haihuwa bisa zargin kashe mijinta da wuka har lahira.

Mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Aminu Ahmed, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Bauchi, ya ce matar ta daba wa mijinta wuka ne bayan wani rikici da ya barke tsakaninsu a Kofar Dumi da ke wajen birnin Bauchi.

Ya ce: “Da samun bayanan, jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na Dibisional, reshen ‘yan sanda na gari, suka yi gaggawar garzaya zuwa wurin da laifin ya faru a adireshin.

“Sun tafi da wanda aka kashe da wanda ake zargin zuwa Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi domin kula da lafiyarsu.

“Saboda haka, rahotannin da aka samu daga likitocin kiwon lafiya sun tabbatar da cewa wanda aka abin ya shafa din ya mutu ne sakamakon rauni da aka yi masa a kirji, yayin da wadda ake zargin ta samu kananan raunuka a jikinta.

“Bincike na farko ya nuna cewa wadda ake zargin, Maimuna Suleiman, ta daba wa mijinta, Aliyu Mohammad wuka, a daidai wannan adireshin ranar 5 ga watan Yuli, da misalin karfe 1800 a gidan aurensu.

“Lokacin da ake yi mata tambayoyi, wanda ake zargin ta amsa laifin da ta aikata.

“Kwamishanan ‘yan sanda, Auwal Mohammad, ya bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jiha (SCID) domin gudanar da bincike don kara bankado al’amuran da suka shafi mutuwar wanda aka kashe.

“Ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala shi.”