Labarai

An Cafke Matashin Da Ya Cire Idon Almajiri Domin Yin Layar Zana

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wani matashi ɗan shekara 17, Isah Hassan, mazaunin Dantsinke layin Rimin Hamza a Ƙaramar Hukumar Tarauni, bisa zargin cire idanun wani almajiri, ɗan shekara 12, mai suna Mustapha Yunusa.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba da daddare, ya ce an kama yaron ne a ranar Talata, da taimakon ƴan sintiri na unguwar.

Ya ce a ranar 20 ga watan Maris ne su ka samu korafin cewa wani da ba a san ko waye ba ya ƙwaƙule wa almajirin idon sa na dama.

Da ga nan ne, a cewar Kiyawa sai Kwamishinan Ƴan Sanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya baiwa rundunar Puff Adder umarnin a nemo wanda ya yi aika-aikar.

Ya ƙara da cewa bayan an dau lokaci a na bincike, sai rundunar ta samu damar cafke Hassan, wanda ya amsa laifin sa cewa wata tsohuwa ce ta ce ya samo idon mutum ta haɗa masa layar zana.

A cewar wanda a ke zargin, ya ce ya samu abokin sa ɗan shekara 16 ne, Sani Abdulrahman cewa yana so a yi masa layar zana, shine shi kuma ya kai shi wajen kakarsa, Furera Abubakar domin ta haɗa masa layar.

Hassan ya ce da ya same ta, sai Furera ta ce ya samo idon mutum a matsayin sinadarin da za ta haɗa masa layar zanan, shine shi kuma ya ja wannan yaro zuwa wani jeji, inda ya ɗaure masa hannaye, ya kuma saka wuƙa mai kaifi ya ƙwaƙule masa idanu na dama.

Ya ƙara da cewa bayan ya kawo mata, idanun, shi ne Furera ta ce sai tabbata Naira 500 ladan aikin da za ta yi masa, sai Hassan ɗin ya ce bashi da Naira 500 amma zai kawo mata idan ya samu, inda ita kuma tsohuwar ta ce ya je ya ajiye idanun.

A ƙarshe dai duk an kame su, inda Kiyawa ya ce za a kai su kotu idan an kammala bincike.

Advertisement