Lafiya

Amfanin Shan Ruwa Tun Da Safe Idan Kun Tashi Daga Barci

Yawancin lokaci safiya na cike da ayyuka da yawa, wanda ke sa mu yi watsi da muhimmin abubuwa da ya kamata mu fara yi idan muka tashi da safe.

Wannan muhimmin abu shine ruwan sha kuma dole ne a shau su akai-akai don samun sakamako walwala da sukuni.

Ruwa ya mamaye kusan kashi 70% na jikin mu don haka, akwai buƙatar mu mu sha ruwa masu yawa a cikin tsarin mu don kada mu ji kishirwa.

Wataƙila ba mu san abin da ruwan da muke sha da safe yake yi ga lafiyar mu ba. Wannan yasa aka hada wannan batun don taimaka mana mu fahimci dalilin da yasa ya kamata mu sha ruwa nan da nan idan mun farka daga barci.

Shan ruwa nan da nan in muka tashi barci yana taimakawa wajen inganta metabolism. Ta yin haka, muna taimaka wa tsarin mu na narkar da abinci ya zama mai ƙarfi da lafiya.

Kamar yadda muka riga muka sani, ruwa yana taimakawa wajen narkewa kuma yana taimakawa abinci don yaduwa a cikin jikin mu da sauri.

Ana iya samun reflux na acid a cikin rufin ciki musamman ga masu ciwon ulcer, wanda zai iya haifar da ƙwannafi da ci.

Shan ruwa da farko idan aka farka zai taimaka wajen hana hakan ta hanyar cire acid a cikin ciki da kuma tsoma shi.

Wataƙila mun sani cewa ruwa shine tsabtace jiki na halitta wanda ke taimakawa wajen fitar da gubobi daga jiki. Kamar yadda yake yi wa acid a ciki, haka nan kuma zai taimaka wajen wanke koda domin gujewa ciwon koda, kamuwa da mafitsara da sauran cututtuka.

Wani dalili na kiwon lafiya da ya sa muke bukatar shan ruwa da safe shi ne, yana taimakawa wajen karfafa garkuwar jikinmu da kuma hana mu yawan kamuwa da rashin lafiya.

Bayan karanta wannan labarin, ina fata za ku yi amfani da safiya ta hanyar shan ruwa da farko?. An shawarce mu mu zauna aƙalla minti 30 kafin mu ci karin kumallo.