Lafiya

Amfanin Hayakin Ganyen Gamji Da Saiwar Tumfafiya 18

Barkan mu da sake saduwa,a yau kuma mun zo maku da wani sahihin maganin gargajiya mai matukar fa’ida, maganin da ba kowa keda ilmi kan alfanin shi ba.

A nemi ganyen gamji dai dai misali, sai a nemo saiwar tumfafiya a tafin hannu haka ba yawa, sai a shanya su bushe, idan sun bushe sai a nemi garwashi a kasko a tirarawa jiki domin:

1. Maganin kumburin jiki adalilin iska.

2. Yana maganin ciwon kai na iskan daji.

3. Domin maganin ha6o (nose bleeding)

4. Domin maganin tsananin ciwon kai na ba gaira ba dalili.

5. Domin maganin kaikayin jiki da kurajen jiki na iskan daji

6. Domin maganin fargaba da jin tsoro da firgita a cikin bacci.

7. Domin kone iskan da ya lailaye jiki Wanda aka turo ta sihirce sihirce.

8. Yana maganin kambun baka da kambun ido

9. Yana maganin cizon kunama sai a marmasa gishiri kadan a kwa6a garin a shafa a inda kunama ta ciza.

10. Shi kuma cizon maciji ana nemo man kade a gauraya da garin a shafa a inda maciji ya ciza.

11. Hayaqin yana korar miyagun kwari a gida.

12. Yana maganin miyagun iskoki da suka addabi gida.

13. Yana maganin cizon kare mai dafi,sai a dake ganyen a shafa da Vaseline,take dafin zai karye.

14. Yana maganin tsananin rashin lafiyar ta6in hankali.

15. Yana maganin kaikayin jiki da fesowar kuraje a fatar jiki

16. Yana kone mugun aiki ko sihirin da aka bizne a gida ko a wajen aiki.,sai a tirara a inda ake zama kamar a gida ko wajen aiki ko kasuwanci.

17. Yana maganin namijin dare ga mace.

18. Ana tirara jiki da shi dayardar Allah za a samu kariya kan sammu da jefe jefe na miyagun mutane.

Mun yi izini ga kowa yayi share domin yan’uwa su amfana