Lafiya

Alamomi ’23’ Da Mace Za Ta Gane Cewa ‘ALJANI’ Ya Aure Ta

  • Yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi a ciki.
  • A duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al’adar ta ba ne.
  • Jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida.
  • Suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta ba.
  • Matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.
  • Kin yarda da jima‘i.
  • Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijin ki ko da wata siffa daban.
  • Yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da taron suna.
  • Ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa a cikin ki ta ya fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki.
  • Yawan yin barin ciki ba tare da wani sanannendalili ba.
  • Yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke.
  • Jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yanadada girma, amma in likitoci suka auna za su ce basu ga komai ba.
  • Rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai.
  • Tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha’awar wasu mazan.
  • Jin wari mara dadi yana fito miki ko ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen gaba.
  • Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman auren ta to in ya tafi ba zai dawo ba.
  • Idan mutum ya dage yana so ya aure ta ita kuma sai ta ji ta tsane shi.
  • In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suy mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take musu.
  • Za ta dinga yawan zaman a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane.
  • Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa.
  • Yawan ciwon kai da yin jiri.
  • Faduwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa.
  • Idan mace ta fara barci sai ta ji an zungure ta ta farka.

Advertisement