Aisha Da Khadija: Marayu Ƴaƴan Marayu
Dole Idanuwan masu imana da tausayi su zubar da hawaye idan suka san irin yanayin da wadannan marayun Aisha da Khadija suka tsinci kan su a ciki.
Idanuwa na basu taba gani, ko jin labarin marayu marasa gata a duniya ba kamar wadannan yan matan biyu da kuke a cikin wannan labarin.
Asalin mahaifiyar wadannan marayin sunan ta Malama Ruqayya, wacce ita ma tsintar ta da aka yi tun tana ƴar jaririya, aka kai ta gidan marayu dake “Tukur Tukur” a cikin birnin Zazzau a Zaria, jihar Kaduna.
Mahaifin yaran shine Malam Tukur, wanda shima asalin shi maraya ne, domin tsintar shi aka yi tun yana ɗan jariri kuma aka kai shi gidan marayu dake Zaria.
Bayan Mallam Tukur da Malama Rukayya sun girma sai aka hada su aure a tsakanin su (Marayi) “Tukur da Rukayya”.
Mal. Tukur da Malama Rukayya sun kasance cikin wata rayuwa da ba abin da za’a ce sai hamdala ga Ubangiji.
Suna cikin zama irin na mata da miji, yau da gobe rashin lafiya ya kama Mal. Tukur bayan sun haifi yaran su biyu mata, Aisha da Khadija, daga karshe kuma Allah ya dauki abin ran Mal. Tukur wanda anan ne labarin A’isha da Khadija ya soma.
Cikin ikon mai kowa, mai komai (Allah), Rukayya ba dangin uwa ba na uba, ba miji sai marayu guda biyu a gaban ta.
Babban abin tashin hankali anan shine, wane ne zai biya musu kudin haya? Abincin su? Makarantar yaran? Da sauran lalurorin su yau da gobe?
Bugu da ƙari, ranar Sallah ina za su je ziyara da yawon Sallah?
Lallai, hakika, babban abin da zai daga hankalin masu tsoron Allah da tausayi shine, alamu na nuna mahaifiyar marayun nan bakin ciki da damuwa yana neman ya zautar da ita (ta fita a hayyacin ta).
Gaskiyar magana yan uwa masu imani, wadannan marayun A’isha da Khadija suna cikin matsanancin halin rayuwa da suke bukatar taimakon al’umma ga baƙi daya.
Da fatan yan uwa zamau taimaka mu yaɗa wannan sakon har ya isa ga kunnen da zasu iya tallafawa waɗannan marayu.