AFCON: Za’a Nuna Wasannin Gasar Cin Kofin Afrika Na 2023 A DSTv Da GOTv

Tashoshin SuperSport na DSTV da GOtv yanzu za su rika watsa dukkan wasanni 52 na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023 da zasu gudana a kasar Cote d’Ivoire.

An tabbatar da hakan a cikin wani sakon Twitter a yammacin Laraba.

Sakon ya ce: “Ba kwa bukatar komai! Kalli dukkan wasanni 52 na #afcon2023 akan
@supersports.”

A makon da ya gabata, Multichoice ya ce DSTV ba zai iya watsa shirye-shiryen AFCON ba.

A wata sanarwa da suka fitar, sun tabbatar da cewa kamfanin bai samu hakkin ba.

Koyaya, SuperSport tare da NTA, za su haskaka gasar kai tsaye daga Cote d’Ivoire.

AFCON 2023 za ta fara aiki a ranar Asabar, 13 ga Janairu, 2024.