Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Girgizar Kasa A Turkiyya Sun Kai Dubu 33

Masu aikin ceto sun sami karin wadanda suka tsira a cikin baraguzai jiya Lahadi, ciki har da wata mata mai juna biyu da yara biyu, a bala’in girgizar kasar da ya kashe mutane sama da 33,000 a Turkiyya da Siriya.

Adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin awo 7.8 da 7.5 da ta afku tsakanin sa’o’i tara a kudu maso gabashin Turkiyya da arewacin Siriya ya kai 33,185 kuma an tabbatar da karuwar gawarwaki.

Yayin da bacin rai ya haifar da fushi a jinkirin ceton da aka yi, an mayar da hankali ga sanya laifi.