17 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Ɓace A Zaftarewar Kasa A Congo

Akalla mutane 17 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu da dama suka bata sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a arewa maso yammacin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Lahadin da ta gabata.

A cewar jami’an agajin gaggawa, bala’in ya afku ne a gabar kogin Kongo a garin Lisal da ke arewa maso yammacin lardin Mongala inda wadanda abin ya shafa ke zama a gidajen da aka gina a gindin wani dutse.

Jami’an sun yi gargadin cewa adadin na iya karuwa yayin da masu aikin ceto ke ta totsa baraguzan da ke karkashin gidajen da suka rushe.

Matthieu Mole, shugaban wata kungiyar farar hula, Forces Vives, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai na cikin gida, ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haddasa zabtarewar kasa.

Mole ya kara da cewa, “Gwamnawar mamakon ruwan sama ta yi barna sosai, ciki har da zaftarewar kasa da ta lakume gidaje da dama.”

Ya kara da cewa “har yanzu adadin wadanda suka mutu na wucin gadi ne saboda har yanzu gawarwakin na karkashin baraguzan ginin.”

Gwamnan yankin, Cesar Limbaya Mbangisa, wanda ya yi jawabi a wani taron manema labarai, ya ce ana matukar bukatar injina da za su taimaka wajen kawar da tarkace da kuma kokarin ceto duk wanda ya tsira.

Mbangisa ya kuma ayyana kwanaki uku na safe a duk fadin lardin.