Labarai
Ɗan Wasan Barkwanci, Kamal Aboki, Ya Rasu A Hatsarin Mota
Shahararren dan wasan barkwanci kuma skit, Kamal Aboki,
ya mutu a wani mummunan hatsarin mota.
Arewa Times Hausa, ta tattaro cewa Aboki na kan hanyar shi ta zuwa Kaduna daga Maiduguri a lokacin da ya yi hatsari a kusa da Gaya a Kano ranar Litinin.
An san marigayin a matsayin tauraro mai tasowa a tsakanin ’yan wasan barkwanci da masu yin sket na arewacin Najeriya.