Labarai

Ɗaliban Jami’ar Katsina Maza Sun Kashe Ɗan Uwansu Akan Ɗaliba Mace

Wani dalibin Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma (FUDMA) da ke Jihar Katsina, wanda aka bayyana sunansa da Abubakar ya rasu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin dalibai kan wata abokiyar karatunsu mace.

Wanda aka kashen dalibi ne mai mataki 200 a Sashen Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar har zuwa rasuwarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce an kama wasu dalibai shida na makarantar kan lamarin da ya faru a unguwar Darawa da ke karamar hukumar Dutsinma a ranar Alhamis.

Lamarin dai a cewarsa ya biyo bayan cece-kuce tsakanin daliban ne.

Kakakin yayi watsi da ikirarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa mutuwar dalibin ta biyo bayan rashin jituwa ne kan addini sannan ya bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da jita-jitar.

Sadiq ya ce: “Hukumar tana aiki tukuru don tattarawa da kuma nazarin dukkan shaidun da ake da su, gami da shaidun gani da ido da nufin samar da cikakkiyar fahimtar abubuwan da suka faru tare da tabbatar da ka’idojin adalci da gaskiya.

“Yayin da bincike ke ci gaba, za a bayyana sabbin bincike ga jama’a don tabbatar da gaskiya.

“Muna karfafa wa duk wani mutum da ke da bayanan da suka dace game da lamarin da zai taimaka wajen gudanar da bincike don ci gaba, saboda duk bayanan da aka samu za a bi su da cikakken sirri.

“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, yayin da yake kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, yana mika ta’aziyyarsa ga ‘yan uwa da abokan arziki da wannan bala’i ya shafa da kuma mahukuntan jami’ar tarayya ta Dutsinma.

“Muna mika juyayinmu da goyon bayanmu a wannan mawuyacin lokaci.”