Ƴan Sandan Najeriya Sun Cafke Wata Tunkiya Bisa Laifi Sata
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno da ke Maiduguri ta cafke tare da tsare wata tunkiya ita kadai da ‘ya’yan ta guda biyu sakamakon korafin da ta yi na cewa ta ci tulin soyayyen kifi da aka baje domin sayarwa.
Lamarin ya faru ne a unguwar Bulabulin dake cikin karamar hukumar Maiduguri a ranar Asabar
An ce har yanzu ana tsare da tumakin da ragunan har yau safiyar Lahadi.
Kamen dai ya biyo bayan wani korafi da wani mai suna Yusuf Ibrahim da ke sayar da kifin ya kai hedikwatar ‘yan sanda na Bulabulin.
A cewar Zagazola Makama, wani masani kan yaki da tada kayar baya kuma manazarci kan harkokin tsaro, Ibrahim ya koka da cewa tun shekaru da dama ne tunkiyar ke ‘ addabar shi.
Ya ce ya shafe shekaru biyar yana jure kutsawa da aikata laifin da dabbar ta yi, amma abin da ta yi a ranar Asabar ya janyo masa hasara mai yawa.
Ibrahim ya cigaba da cewa tunkiyar ta zama dabi’a ta zagaya shagon shi tare da yin hakuri tun da dadewa yayin da yake soya kifi.
“Sai kuma da hankali na ya karkata, tunkiyar ta yi takuri zuwa teburin kuma kafin in ankara ta, ta ci da yawa daga kafin in kore ta,” in ji shi.
Ya kara da cewa ya hakura har tsawon shekaru biyar kuma ya bukaci mai shi da ya dauki mataki ta hanyar sayar da ita. Sai dai yace koke-koken nasa bai yi nasara ba.
Mai tumkiyar, wata Luba Mohammed – uwar gida, ta koka da cewa ba ta san yadda da kuma lokacin da tumakin suka fara son soyayyen kifi ba.
Ta yarda cewa mai sayar da kifi ya yi mata ƙara a cikin shekaru da yawa game da abin da tumakin suka yi.
Matar ta roki Ibrahim da yayi adalci da rahama ya sako tunkiyar, tare da yi mai alkawarin cewa za ta sayar, ko ta yanka ta.