Labarai

Ƴan Boko Haram Sun Tarwatsa Wayoyin Da Ke Kai Wutar Lantarki Borno

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun sake kai hari a kan babbar tashar wutar lantarki ta National Grid, da igiyoyi da wayoyi, lamarin da ya jefa birnin Maidugurin jihar Borno ga-baki daya cikin duhu, bayan da rahotanni suka ce sun kai harin bam a wasu sandunan wutar da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Wani babban jami’in tsaro da ke sintiri a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ya ce, “Mun kuma yi mamakin ganin wasu tasoshin wutar lantarki a kasa kuma igiyoyin sun fado a tsakaninsu a wani wuri mai nisa tsakanin Mainok da kauyen Jakana a yayin da muke sintiri a ranar Juma’a da safe, abin da yasa muka ja hankalin sauran jami’an tsaro da jami’an wutar lantarki su sani.

“Eh, mun yi kokarin isa wurin amma ba za mu iya zarce zuwa wurin da lamarin ya faru ba domin bisa ga dukkan alamu harin bam ne kuma yana da hatsarin isa wurin ba tare da na’urorin kariya da bama-bamai ko wurin aiki ko na’urar gano wadanda ba su tashi ba, Na’urorin fashewa (IEDs).”

Jaridar Blueprint ta tattaro cewa, a wani kauye mai nisa, Katsaita, mazauna yankin sun ga wata fashewa babba da ta biyo bayan wani haske mai kama da walƙiya a daidai lokacin da wutar lantarki ta yi bastin.

“‘Yan ta’addar Boko Haram ne suka yi amfani da wani bam suka ruguza daya daga cikin caben,” in ji wani mazaunin garin da ya bayyana kansa a matsayin Nasiru.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Manajan Hulda da Jama’a na Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), Mista Ndidi Mbah, ya ce abin da ya faru na baya-bayan nan aikin barna ne, ya kara da cewa, “Tuni injiniyoyin TCN sun koma wurin inda suka gano shaidar hakan, abubuwan fashewa da aka yi amfani da su wajen kai harin. An shirya wani dan kwangila don fara aikin sake ginawa.”