Ƴan Arewa Najeriya Sun Zargi BBC Hausa Da Bangaranci

Mazauna Arewacin Najeriya sun zargi kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa da nuna bangaranci wajen yaɗa labarai da rahotanni.

Idan ba’a manta ba, a yan kwanakin nan da suka gabata, wani mawakin Kudancin Najeriya mai suna Mohbad, ya mutu cikin wani yanayi mai rikitarwa, wanda har yanzu yan sandan kasar na ci gaba da bincike akan mutuwarsa.

Bayan mutuwar Mohbad, dubban mutane a Kudu da sauran sassan kasar sun gudanar zanga-zangar neman hukumomi su bankaɗo mutanen da ke da hannu wajen mutuwar mawakin domin su fuskanci shari’a.

Zanga-zangar dai ta shiga shafukan intanet da dama, ciki har da sashen Hausa na BBC.

Sai dai bayan wallafa abubuwan da suka gudana a zanga-zangar ta Mohbad a shafukan ta na sada zumunta, wasu mutanen Arewacin Najeriya musamman masu amfani da shafukan sada zumunta kamar Facebook da Twitter (wacce ake kira X a yanzu), sun yi zargin cewa BBC Hausa ta kauda kai daga wata zanga-zangar lumana da ta gudana Arewa.

Akan wannan dalilin, al’ummar Arewa, suka yi ƙira ga BBC Hausa kan cewa nan da awanni 24, idan basu ɗora zanga-zangar lumana da al’ummar Arewacin Najeriya da Suke yi ba a shafukan su na sada zumunta, zasu daina bibiyar labaran su ga baƙi ɗaya.