Ƙungiyar RSF Ta Sudan Ta Kashe Mutane Sama Da 1,290 A Darfur

Ƴan kungiyar Rapid Support Forces (RSF) ta kasar Sudan sun yi wa sansanin ‘yan gudun hijira kawanya a ranar 2 ga watan Nuwamba bayan sun kai hari a wani sansanin soji da ke yammacin Darfur. A cikin kwanaki uku masu zuwa, kungiyar ‘yan ta’addar ta aikata wani abu da zai kai ga kisa mafi girma tun bayan barkewar yakin basasa a watan Afrilu.

Masu sa ido na cikin gida sun shaidawa Al Jazeera cewa kimanin mutane 1,300 ne suka mutu, 2,000 suka jikkata, yayin da wasu 310 suka bace.

Montesser Saddam, wanda da kyar ya tsallake rijiya da baya, ya isa kasar Chadi a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce: “Sun tafi gida gida don neman maza kuma suka kashe duk wanda suka samu.” “Akwai gawarwaki da yawa a kan tituna.”

Wannan ta’asa na baya-bayan nan dai wani bangare ne na yakin da kungiyar RSF da kawayenta ke yi na kawar da kabilar Masalit da ba Larabawa ba daga yammacin Darfur, a cewar masu fafutuka da wadanda suka tsira da rayukansu.

Tun bayan barkewar yakin basasar Sudan, Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin kasashen yammacin duniya sun yi Allah-wadai da kashe-kashen da ake yi wa Masalit daga kasarsu. Sai dai suka da damuwa ba su hana RSF aiwatar da karin ta’asa ba.