Labarai
Ƙazamin Faɗa Na Gudana A Kusa Da Asibitin Al-Shifa A Gaza
Wani mai fafutuka a asibitin Al-Shifa ya bayyana halin da ake ciki a yanzu a matsayin “mai matukar wahala”, yana mai cewa “gagarumin fada” na faruwa a kusa da ginin.
A cikin wani faifan bidiyo da ya yada a shafukan sada zumunta, an ga hayaki yana ta turnukewa a bayan asibitin yayin da fashe-fashe da harbe-harbe ke haskaka sararin samaniya.
Rikici yana faruwa a “arewa, a al-Shati [sansanin ‘yan gudun hijira], da kuma kusa da Al-Shifa. Wannan ya yi kusa sosai,” in ji shi.
Ya kara da cewa “A halin yanzu muna fagen fama, wannan yankin yaki ne wanda ya sha bamban da yakin Gaza.” “Yakin zalunci ne.”
Ya kara da cewa karar tashin bama-bamai na ta kara kamari a cikin sa’o’i biyu da suka gabata, yana mai jaddada cewa ba a yi shiru na minti daya ba.