Yan Sanda Sun Cafke “Fatalwa” Mai Damfarar Mutane Kudi A Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da cafke wani mutum mai shekaru 59, Muhammad Abubakar aka Malam Sabo, wanda yake yin kama da fatalwa domin damfarar jama’a.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X da aka tabbatar a daren ranar Talata.

A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya saba da 419 wanda ya kware wajen damfarar jama’a ta hanyar da ba ta dace ba.

“Mafi yawa, wanda ake zargin yana ɓoye ainihin sa, yana yin kamar fatalwa ne, yana magana da waɗanda abin ya shafa da muryoyi daban-daban.

“Wanda ake zargin, a wasu lokuta yakan canza sautin muryarsa zuwa na mace ko yaro domin ya yaudari wadanda abin ya shafa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kwanan nan ya yaudari wani Abba Bale na Demsawo na kudi dubu dari uku (N300,000.00)”