Tarihi

Tarihi: Abacha Ya Tseratar Da Rayuwar IBB A Lokacin Gagarumin Juyin Mulkin 1990 Da Bai Yi Nasara Ba

Daya daga cikin shugaban kasar da ke da cece-kuce, Janar Sani Abacha ba shi da mugun nufi kamar yadda mutane da yawa ke zato. Ƙarƙashin rigar mulkin shi na danniya akwai abokin aminci, mai kishin ƙasa kuma ƙwararren soja. A gaskiya mutane da yawa suna kallon shugabancin shi a matsayin daya daga cikin mafi zubar da jini a zamanin shugabancin ‘Jack and boots’ wanda ya mulki kasar daga ranar 15 ga Janairu, 1966 har zuwa Mayu 1999.

Kamar yadda wani mashahurin masanin falsafa ya taba cewa, ”Ko a jahannama, akwai waliyyai”, wannan ma’anar ya fi dacewa da sharuddan magana game da Janar Abacha wanda ya karbe ragamar mulki da karfin tsiya daga shugaba mai ci Ernest Shonekan a watan Agustan 1993 har zuwa lokacin da ya mutuwa a watan Yuni 1998 bayan kamuwa da ciwon zuciya.

Duk da haka, mutumin da ke bayan inuwar har yanzu ana girmama shi a tsakanin wasu ɓangarorin a matsayin wanda ya taimaka wajen ɗaga fuskar al’adun mu ta hanyar shirye-shiryen wayar da kan jama’a da dama da gwamnatin shi ta fara. An kuma san shi da sake fasalin fagen wasanni a cikin ƙasar tare da Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Dream Soccer wanda a tarihin ta lashe zinare a gasar Olympics ta 1996 a ƙwallon ƙafa da kuma rawar da ya taka a lokacin gasar cin kofin duniya ta Amurka 1994.

A baya-bayan nan, manufofin tattalin arzikin Sani Abacha sun taimaka wajen bunƙasa ayyukan gida da kuma cigaba da samun hauhawar farashin kayayyaki tsakanin 1993-1998. A lokacin mulkin shi, kasar ta yanke hulda da manyan kasashen duniya a wani yunkuri na bunkasa masana’antu a cikin gida wanda zai zama ingantacciyar hanyar maye gurbin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje.

Kada kuma mu manta cewa a lokacin da kujerar mulkin da ke Dodan Baracks, Obalende, Legas ke fama da tashin bama-bamai da masu yunkurin juyin mulki karkashin jagorancin wani Manjo Orkar, shi ma Abacha da gwamnatin shi ne suka fafata da su har suka tsaya cak. .