Labarai

Ruftawar Ginin Makarantar A Jihar Filato: Gwamnati Ta Tabbatar Mutuwar Mutane 22

Gwamnatin jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane 22 tare da jikkata wasu 132 a ginin makarantar Jos da ya rufta.

Musa Ashom, kwamishinan yada labarai, ya ce shida daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

Ashoms ya ce wadanda suka jikkata suna karbar kulawa a wasu manyan cibiyoyin lafiya na jihar, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa.

NAN ta ruwaito cewa wani bene mai hawa biyu na makarantar Saints Academy, makarantar sakandare da firamare da ke unguwar Busa-Buji da ke karamar hukumar Jos ta Arewa, ya rufta inda ya ruguje akan dalibai, malamai da sauran su.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Juma’a a lokacin da daliban ke rubuta jarabawar zango na uku.

A halin da ake ciki, Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan rashi da kuma babban rashi ga jihar.

Mutfwang ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Mista Gyang Bere, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a ya fitar ranar Juma’a a Jos.

Gwamnan wanda ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, ya kuma bayyana lamarin a matsayin abin takaici da sakaci.

“Wannan abin takaici ne, abin bakin ciki, mai ratsa zuciya. Mun yaba da yadda jami’an bincike da ceto suka shiga tsakani a kan lokaci, da kuma jama’a, wadanda suka garzaya harabar makarantar domin taimakawa wajen kwashe wasu dalibai da ma’aikatan da suka tsira,” inji shi.