Labarai

Rasha Ta Mayar Da Martani Kan Amfani Ɗaga Tutar Ƙasar Da Masu Zanga-Zanga Ke Yi A Najeriya

Ofishin jakadancin kasar Rasha a Najeriya ya musanta cewa yana da hannu da wata kungiyar masu zanga-zanga a arewacin Najeriya da aka gani suna kaɗa tutocin kasar Rasha.

DAILY POST a baya ta ruwaito cewa, an ga masu zanga-zanga a wasu sassan kasar suna maci kan tituna, suna daga tutocin kasar Rasha, suna rera take, yayin da wasu ke rike da alluna masu dauke da sakonni daban-daban.

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kuma tabbatar da kama wani tela a jihar Kano da ke ɗinka tutocin kasar Rasha.

Hukumar ta kuma ce ta kama wanda ake zargin tare da masu daukar nauyinsa.

Sai dai a wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar ta ce Rasha ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ciki har da Najeriya.

Ta ce abin da masu zanga-zangar suka yi bai nuna wata manufa ko matsayi na gwamnatin Rasha ba.

Sanarwar ta ce, “Ofishin Jakadancin ya lura da rahotannin da kafafen yada labarai na Najeriya ke yadawa da kuma yadda ake yada bidiyo da hotuna a kafafen yada labarai na zamani da ke nuna masu zanga-zangar a jihohin arewacin kasar dauke da tutocin kasar Rasha suna rera taken shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

“Gwamnatin Tarayyar Rasha da kuma duk wani jami’in Rasha ba sa hannu a cikin waɗannan ayyukan kuma ba sa daidaita su ta kowace hanya.

“Kamar yadda aka saba, muna jaddada cewa Rasha ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashen waje ciki har da Najeriya. Wadannan aniyar wasu masu zanga-zangar na daga tutocin Rasha zabi ne na daidaikun mutane, kuma ba sa nuna wani matsayi ko manufofin gwamnatin Rasha kan batun.

“Muna mutunta dimokaradiyyar Najeriya kuma mun yi imanin cewa zanga-zangar lumana da ta dace da dokar Najeriya alama ce ta dimokradiyya. Duk da haka, idan waɗannan abubuwan sun haifar da duk wani rikici ko tashin hankali mun yi Allah wadai da su.”