Addini

Mene Ne Hukuncin Fitar Digon Maniyyi Bayan An Yi Wanka?

Bayan wankan janaba, idan mutum ya ga digon ruwan maniyyi ya fito a al’aurar sa, shin zai sake wankan? Ko dai ya wanke digon maniyyin kawai zai yi?

Idan mutum ya fitar da maniyya ba tare da wata sha’awa ba, ba sai ya sake yin wanka. Ibn Qudaamah (rahimahullah) yana cewa: Idan mutum yayi mafarki ko ya yi jima’i, ya fitar da maniyyi, sai yayi wankan janaba, sannan daga baya sai wani maniyyi ya fita daga cikin sa, sanannen magana daga Ahmad ya ce: ba sai ya sake yin wanka ba.

Al-Khallaal ya ce: Akwai riwayoyi da yawa daga Abu ‘Abd-Allaah – watau Imam Ahmad – cewa abin da zai yi shi ne alwala’ ko yayi fitsari ko bai yi ba, kuma wannan shi ne ra’ayin da ya zauna a kai.

Wannan kuma an ruwaito daga ‘Ali, Ibn ‘Abbaas, ‘Ata’, al-Zuhri, Malik, al-Layth, al-Thawri da Ishaq. Sa’eed bn Jubayr ya ce: “Ba lallai ba ne yayi sake wani wanka ba, sai dai idan hakan ya kasance tare da sha’awa.