Labarai

Mali Ta Katse Hulɗa Da Ƙasar Yukiren Bisa Harin Da Aka Kaiwa Sojojin Hayar Rasha, Wagner

Kasar Mali ta sanar da katse huldar diflomasiyya da kasar Ukraine, inda ta zargi wani babban jami’i da amincewa da rawar da Yukiren ta taka a wani gagarumin hari a watan Yuli wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin haya da dama na kungiyar Wagner ta Rasha da kuma sojojin Mali.

‘Yan tawayen Abzinawa na arewacin kasar sun ce sun kashe sojojin haya akalla 84 da sojojin Mali 47 a cikin kwanaki uku da suka kwashe ana gwabza fada a karshen watan da ya gabata a arewacin kasar da ke yammacin Afirka, a wani mataki na shan kaye mafi muni da Wagner ta fuskanta tun bayan da ta shiga rikicin shekaru biyu da suka gabata.

A ranar 29 ga watan Yuli, Andriy Yusov, mai magana da yawun hukumar leken asirin sojin Ukraine (GUR), ya shaidawa kafar yada labarai ta Suspilne cewa ‘yan tawayen Mali sun samu “dukkan bayanan da suke bukata, wanda ya ba su damar gudanar da aikinsu akan masu aikata laifukan yaki na Rasha”.

Mali ta ce ta samu “cikin matukar kaduwa” na kalaman kuma Yusov “ya amince da hannun Ukraine a cikin wani harin matsorata, mayaudara da dabbanci daga kungiyoyin ‘yan ta’adda masu dauke da makamai wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an Wagner da tsaro na Mali”.

Ta ce za ta wargaza dangantakar “da sauri”, in ji wata sanarwa daga kakakin gwamnatin Kanar Abdoulaye Maiga.

Mali ta kuma ba da misali da kalaman jakadan Ukraine a Senegal Yurii Pyvovarov, wanda Senegal ta gayyace shi ranar Asabar kan wani faifan bidiyo da aka buga a Facebook inda Pyvovarov ya ba da “goyon baya maras tabbas da rashin cancanta ga harin ta’addanci” a Mali.

Ayyukan da Ukraine ta yi ya keta ‘yancin Mali kuma ya zama katsalandan da ba a yarda da shi daga kasashen waje da goyon bayan ta’addanci na kasa da kasa, a cewar Maiga.